EFCC ta gurfanar da alkalin babban kotu bisa zargin karbar rashawa

Hukumar EFCC ranar Laraba a babban birnin tarayya Abuja ta gurfanar da wani babban Alkalin Kotun Najeriya Justice Yunusa a gaban Kotu bisa zargin cin hanci da rashawa.

Justice Yunusa ya gurfana a gaban babban Kotu a Abuja tare da Esther Agbo wata ma'aikaciyar Lauya mai zaman kansa Rickey Tarfa a bisa zargi kan  laifuka biyar a gaban Justice S.O. Solebo.

Ana zargin Justice Yunusa da karban kudin toshiya daga manyan Lauyoyi Joseph Nwobike da Rickey Tarfa domin a karkatar da gaskiya. Haka zalika ana zargin cewa Justice Yunusa ya karbi N1.5m daga Joseph Nwobike domin ya karkatar da gaskiya.

Wasu karin bayanai sun nuna cewa Justice Yunusa ya karbi N700.000 daga Nwobike a 2015, EFCC ta ce haka kuma Justice Yunusa ya karbi N1.5m daga Esther Agbo wacce ke aiki da Lauya Rickey Tarfa domin Justice Yunusa ya karkata gaskiya.

Justice Yunusa da Esther Agbo basu amsa laifinsu ba kuma ana tattauna yanayi na yiwuwar bayar da belinsu kafin mu rubuta wannan labari.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN