Bata gari sun kashe jami'in NSCDC har lahira yayin da yake aiki

Wani jami'in rundunar NSCDC a jihar Sokoto ya rasa ransa yayin da yake bakin aiki sakamakon artabu da rundunar hadin gwuiwa na jami'an tsaro suka yi da wasu bata gari da suka kai farmaki a kauyen Kursa/Gobirawa a gundumar Gandi na karamar hukumar Rabah.

Safeto Nafi'u Wamakko ya rasa ransa ne yayin da rundunar hadin guiwar suke kokarin ceto wasu mutum biyu da bata garin suka yi garkuwa da su bayan sun yi gagarumar sata ranar Juma'a 19 ga Janairu.

Rahotanni sun ce barayin sun kashe mutum biyu da basu ji basu gani ba a kauyen kafin su shiga kungurmin daji da mutanen da suka sace tare da kayakin da suka sata, amma jami'an tsaron sun bi su bayan sun sami rahotu, yanayi da ya haddasa harbe harbe da bindigogi da ya kai ga halaka jami'in NSCDC Nafi'u.

Rundunar ta hadin guiwa ta hada da jami'an yansanda,soja DSS da NSCDC. Kwamandan rundunar NSCDC na jihar Sokoto  Alhaji Babangida Abdullahi Dutsinma ya ce wasu daga cikin bata garin sun tsere ne da raunukan harsashi ya kuma roki jama'a cewa su kai rahotun duk wani da suka gani da raunin bindiga ko idan basu yarda da take-takensa ba.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN