Ziyara kan shirin kaddamar da kanbin tsoffin soji a jihar Kebbi

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya karbi bakoncin tawagar sashen harkokin tsofaffin soja na Ma'aikatan tsaro daga babban birnin tarayya Abuja yau a ofishinsa karkashin jagorancin Manjo janar OO. Soleye.

Janar Soleye ya ce sun zo jihar Kebbi ne domin su kaddamar da kanbin tsofaffin sojin Najeriya bayan shuga Muhammadu Buhari ya kaddamar da shi a mataki na tarayya a Abuja 'yan kwanaki da suka gabata.

A yayin da yake mayar da martani a madadin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu, Mataimakin Gwamna Samaila Yombe Dabai ya mika godiyarsa tare da tabbatar ma tawagar da cewa zai isar da sakon su ga Gwamna Atiku Bagudu tare da tabbatar masu da samun goyon baya daga Gwamnatin jihar Kebbi


**************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN