Yombe ya karbi bakoncin matasan soji 'yan Masarautar Zuru (Hotuna)

Isyaku Garba |

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya karbi bakoncin tawagar mutum 30 cikin mutum 165 'yan asalin jihar Kebbi rukuni na 76 da suka kammala samun horo na kasancewa cikakkun sojin Najeriya a Makarantar koyon aikin soja Depot da ke Zaria ranar Juma'a a gidansa da ke Birnin kebbi.Sojin guda 30 sun fito daga kananan hukumomi ne da ke karkashin Masarautar Zuru.

Jagoran tawagar Pte. Anas Mai Dawa ya jagoranci wata kwarya-kwaryar sintirin gabatarwa na karramawa ga Mataimakin Gwamna, inda ya ce sun kawo ziyarar ban girman ne domin su nuna godiya ga Gwamnatin Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu bisa na mijin kokarisa wajen sama wa matasa aikin yi tare da bayar da tallafi da daimako a lokacin horo.

Yombe ya bukaci su kasance masu ladabi da biyayya ga hukumomin soja, sa'anan su kasance masu nuna halaye na gari domin su fito da kyakkyawar sun jihar Kebbi.

Ya kara da cewa kamar yadda suka gani, Gwamnatin Atiku Abubakar Bagudu ta mayar da hankali ne wajen inganta rayuwar matasa da taimaka masu wajen bunkasa sana'oi a fadin jihar Kebbi.haka zalika ya yaba ya Gwamna Atiku Bagudu bisa bayar da kwangilar gina filayen wasa a Masarautu hudu da ke fadin jihar Kebbi.

Sharhabila Hassan wacce ta fito daga karamar hukumar Danko wasagu itace mace kwaya daya tilau da ke cikin tawagar.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN