'Yansanda 6 sun mutu yayin wani farmaki a Numan (Munanan hotuna)

Rahotanni da ke fitowa daga jihar Adamawa sun nuna cewa wasu jami'an 'yansanda sun rasa ransu bayan sun yi diran mikiya akan wadansu Fulani da ke kauyen Dowaya kuma suka yi kokarin su kama wasu Manya daga cikin al'ummar ta Fulani.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Adamawa Othman Abubakar ya tabbatar wa Premium Times cewa ya sami labarin cewa akwai matsala a Numan amma bai bayar da wani cikakken bayani ba. Abubakar ya ce yana cikin wani taro ne tare da Kwamishinan Labarai tare da Manyan Mutane da ke ruwa da tsaki a al'amurra ko da labarin ya same shi.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na Arewa maso gabas Mafindi Umaru Danburam ya shaida wa Premium Times cewa ya sami labari cewa "Ma'aikata cikin kaki sun kai hari akan wadanda suka nemi mafaka a Dowaya" ya ce an harbe mutum biyu kuma yana kokarin ya sami kari bayani.

Wannan ya biyo bayan gomman Mata da yara na Fulani da ake zargin wani gungun tsigeru sun kashe a Numan mako daya da ya gabata.

Wata majiya ta ce 'yansanda sun sami bayani cewa Fulani suna taruwa a wani garin tare da niyyar kai farmaki , amma wata majiya kuma cewa ta yi Fulanin suna taruwa ne domin yin makokin 'yan uwan su , mata da yara da aka kashe masu a mako da ya gabata a kauyukan Shafaran, Shawal, Gumara, Kikam da Kadamt.

Hugaban ya kara da cewa "Sakamakon taruwa da Fulani suka yi domin wannan makokin wadansu mutane basu saki jiki ba sai suka sanar da jami'an tsaro wanda su kuma suka yi wa garin diran mikiya cikin dare lamari da ya rikice zuwa kazamin fada da ya kai ga mutuwar 'yansandan kwantar da tarzoma guda shida"

Ya kuma kara da cewa "Yanzu haka an karo jami'an tsaro a Numan da kewaye kuma tuni jama'a na tserewa daga yankin sakamakon wannan tashin hankali"


 **************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN