• Labaran yau

  'Yan Najeriya ne ke sayar da 'yan uwansu 'yan Najeriya a Libya

  Bayan isowar mutum 150 daga kasar Libya da daren ranar Alhamis , wasu karin bayani daga wa'danda suka iso ya nuna cewa 'yan Najeriya ne ke sayar da 'yanuwansu 'yan Najeriya a kasar ta Libya.

  Wata mai aikin gyaran gashin Mata mai suna Odion Saliu mai shekara 26 'yar asalin jihar Edo ta ce an sace ta a kasar Libya aka mika ta ga wani 'dan Najeriya wanda ya tilasta ta kira Mahaifiyarta ta aika da N200.000 amma daga bisani shi 'dan Najeriya da ya karbi kudin ya sake sayar da ita akan Dinar 3,000 komanin N790.000.

  Akwai ire-iren wadannan korafe-korafe daga bakin wadanda suka fuskanci wannan kazamin lamari a kasar ta Libya.

  Bayanai sun nuna cewa 'yan Najeriya da ke fataucin 'yan uwaan su 'yan Najeriya a kasar ta Libya sun fi mugunta ga 'yan uwansu 'yan Najeriya wanda da su ne ake hada baki da Larabawa domin tafiyar da wannan fataucin.


  **************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: 'Yan Najeriya ne ke sayar da 'yan uwansu 'yan Najeriya a Libya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama