• Labaran yau

  Yadda aka yi kusan kashe karuwa da saurayi da suka yi zina kiri kiri a wajen biki

  Wani mutum da wata karuwa a kauyen Umuduru da ke karamar hukumar Ihiala a jihar Anambra sun kure mutuwa sakamakon dukan tsiya da suka sha a hannun mutane a wajen wani bikin bizine gawar wata mace bayan sun yi zina kiri-kiri baro-baro a gaban jama'a da suka halarci bikin bizine gawa lamari da ya harzuka wasu matasa da suka afka wa mazinatan.

  Bayanai sun nuna cewa karuwar ta zo wajen bikin a cikin buguwar barasa ta ce "bari in nuna maku" kawai sai ta tube zindir kuma ta jawo wani saurayi mai suna Chinwuba daga kauyen Ogboro Uumunwaji da ke Ihiala daga cikin taro kuma ta kwanta inda kai tsaye shi kuma ya hau ta ya biya bukata.

  Ganin haka ne ya harzuka wasu matasa da suka afka masu da duka, amma nan take Dattijai suka sa baki suka ceci saurayin yayin da karuwar ta yi batan dabo lokacin da kura ya turmuke sakamakon haya-haya a lokacin da aka fara duka.

  Daga bisani dattijan sun ci saurayin tara cewa zai kawo kwali shida na barasa da wasu kudade da ba'a fayyace adadinsu ba cewa dattijan za su yi amfani da barasan domin gudanar da wasu ka'idodi na al'ada.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda aka yi kusan kashe karuwa da saurayi da suka yi zina kiri kiri a wajen biki Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });