• Labaran yau

  Ya banka wa kansa wuta bayan ya kashe matarsa da ya gada


  An kama wani Magidanci 'dan shekara 37 bisa zargin kashe Matar da ya gada daga wajen 'dan uwansa. Bayanai sun nuna cewa Buba ya yi wa Satina 'yar shekara 45 duka da misalin karfe 4:30 na safiyar 16 ga watan Nuwamba 2017 lamari da ya yi sanadin mutuwar ta. Satina tana da 'yaya hudu wanda suka haifa da tsohon mijinta Danladi.

  Bisa al'adar al'umman garin, Shu'aibu ya gaji Satina bayan rasuwar yayansa kuma an gudanar da tsare-tsare na gargajiya a watan Fabrairu na bana sai suka tare suka fara zama tare a kauyen Kuruduma II a Asokoro na babban birnin tarayya Abuja.

  Kwamishinan 'yansanda na birnin tarayya Muhammed Saddik Bello ya ce Shu'aibu ya sami labari cewa Satina tana nema da wani, amma marmakin Shu'aibu ya yi bincike sai ya kashe ta.

  Ganin tsananin laifin da ya aikata, Shu'aibu ya ruga zuwa cikin kichin ya bulbula wa jikinsa kalanzir ya kyasta wa kanshi wuta daga bisani kuma ya kai kanshi wajen 'yansanda a chaji Ofis na Asokoro.

  Shu'aibu ya shaida wa Manema labarai cewa aikin shedan ne, domin ya san ya aikata abin da bai kamata ba.Ya kuma roki iyalinsa da Iyayen Satina su yafe masa domin ya san ya yi kuskure.

  .
  **************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

  Hoto: sunnewsonline
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ya banka wa kansa wuta bayan ya kashe matarsa da ya gada Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });