• Labaran yau

  Wasu matasa da suka boye bindigogi a jikin su sun fada hannu a tashar mota

  Wasu matasa biyu sun gamu da fushin jama'a da suka harzuka a tashar mota ta Gwagwalada bayan an ga bindigogi a jikin matasan guda biyu da suka yi kokarin  shiga mota zuwa Benin daga Abuja.

  Lamarin ya afaru a tashar mota ta Wazobia da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

  Bayanai sun nuna cewa wani yaron mota da yake yin lodi shi ne ya gan bindigogin da matasan suka boye a jikin su, lamari da ya sa ya fallasa ta hanyar jawo hankalin jama'a game da bindigogin.

  Abin ka da 'dan Najeriya, daga isowar jama'a sai suka afka masu da duka, suka fara kiran su 'yan fashi da makami, sakamakon haka suka yi wa daya daga cikin su rauni kafin 'yansanda suka zo suka cafke su zuwa caji ofis na 'yansanda a Gwagwalada.

  Wata majiya ta labarta mana cewa tuni dai aka mika matasan ga hedikwatar 'yansanda na birnin tarayya domin ci gaba da bincike.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wasu matasa da suka boye bindigogi a jikin su sun fada hannu a tashar mota Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });