• Labaran yau

  Tsohon Gwamna Sa'idu Dakingari da dimbin magoya bayansa sun koma jam'iyar APC

  Isyaku Garba |

  Tsohon Gwamnan jihar Kebbi Alh. Sa'idu Nasamu 'Dakingari tare da dimbin magoya bayansa sun canja sheka daga jam'iyar PDP zuwa jam'iyar APC mai mulki a jihar Kebbi bisa abin da suka kira "Tsarin tafiyar da shugabanci bisa adalci, ci gaba da ya kai ga nassarori a Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi karkashin jam'iyar APC" .

  Bayanin haka ya fito ne a wata sanarwa da ta fito daga hannun Sakataren jam'iyar APC na jihar Kebbi Alh. Sani Dododo wanda aka samu ta kafar sada zumunta.

  Sanarwar ta zayyana sunayen wasu da suka yi fice da suka hada da :

  1- Tsohon Gwamnan Jihar Kebbi Alh. Saidu Usman Dakin Gari.
  2- Tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Ibrahim K. Aliyu
  3- Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi Alh. Garba Rabi'u Musa Kamba
  4- Tsohon Shugaban karamar Hukumar Mulkin Birnin Kebbi Alh. Musa Ibrahim Dan illela
  5- Tsohon Shugaban karamar Hukumar Augie Garba Umar Birnin Tudu
  6- Tsohon Shugaban Karamar hukumar Mulkin Kalgo Alhaji Abubakar Kuka
  7- Tsohon Dan Majalisar Tarayya Hon. Sani Kalgo
  8- Tsohon Dan Majalisar Tarayya na Yanzu Zuru Hon. Dan Alkali Durunbun Zuru
  9- Tsohowar Yan Yan Majalisar Tarayya ta Yankin Yauri Hon. Halima Hassan Tukur
  10-  Alh. Abubakar Sadik Yalwa Katikan Yauri
  11- Ummaru Maye Yauri
  12- Lawali Na Malam Dakin Gari
  13- Alh. Shehu Ma'azu Zuru
  14- Alh. Zayyanu Maigishiri

   Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tsohon Gwamna Sa'idu Dakingari da dimbin magoya bayansa sun koma jam'iyar APC Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });