Mutum 1 ya mutu,1 ya bace,2 suna jinya sakamakon farmakin Fulani a Illo (Hotuna)

Isyaka Garba |

Sakamakon rikici tsakanin Manoma da Makiyaya da ya yi sanadin mutuwar wani Manomi tare da bacewan wani mutum daya yayin da biyu ke jinya a babban Asibiti a kauyen Sabon gari da ke gundumar Illo, wakilin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu wanda Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya wakilta ya bukaci jama'ar wannan Kauye su dakata daga shiga wurin da ake takaddama akai yayin da ya kuma bukaci Makiyaya da suka shigo da dabbobin su domin kiwo su ma su fice daga wurin domin kauce ma fitina kafin Gwamnati ta tabbatar da wanzar da umarnin Kotu akan lamarin.

An zargin cewa ranar Talata wasu Fulani sun shiga wani yanki da dabbobinsu da ake takaddama tsakanin Manoma da Makiyaya a fadamar garin Sabon gari wanda ake zargin cewa dabbobin su yi barna ga amfanin gona sakamakon wani hukuncin wata Kotun Majistare da ta zartar da hukunci akan cewa Manoma su tashi a wurin kafin ranar 19/12/2017.

Bayanai sun nuna cewa cikar wa'adin ke da wuya ranar Talata sai wasu Makiyaya suka shiga wurin da dabbobin su, yanayi da ya kawo takaddama da ake zargin cewa Makiyayan sun yi amfani da bindiga suka harbi wani Manomi mai suna Muhammad Mai gadi wanda sakamakon haka ya rasu, haka zalika wani Manomi mai suna Ali Tela ma ba'a gan shi ba tun jiya talata bayan ya nutse a cikin ruwa sakamakon harbin bindiga, yayin da wani Manomi mai suna Muhammadu Dan Gambo ke kwance tare da wani Manomin suna karbar magani sakamakon raunukan albarushi da aka cire masu a babban Asibitin garin Illo.

Yayin da tawagar Mai girma Gwamnan jihar Kebbi wanda Mataimakinsa Alhaji Samaila Yombe ya wakilta ta isa wurin da lamarin ya faru, an gani zahiri yadda Makiyayan suka mamaye gurin da dabbobin su kuma abun mamaki shine yadda suka ci gaba da harbi mai kara da aka yi amanna cewa sautin harbin bindiga ne duk da kasancewar jami'an tsaro a tawagar Mataimakin Gwamnan da kuma wasu karin jami'an tsaro da ke a gurin wadanda suka raka tawagar.

A wani jawabi da ya yi wa jama'a a Kauyen Sabon Gari, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ya roka , sa'annan ya bukaci duk bangarorin biyu su rungumi hakuri kuma su kaurace ma gurin da ake takaddama akai kuma a jira mataki da Mai girma Gwaman jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu zai dauka akan lamarin, wanda ya ce zai tattara bayanai akan lamarin domin gabatarwa ga Gwamna.

Sarkin Illo Alh. Muhammadu Wankwai ya yi jawabi ga tawagar ta Mataimakin Gwamna inda ya roki Gwamnatin jihar Kebbi ta shiga tsakani domin kawo karshen yawan rikici da ke kai wa ga zubar da jini har da rasa rayuka kamar yadda ya faru a garin Sabon gari ranar Talata sakamakon takaddama akan wannan gurin a garin Sabon gari.

Daga cikin jami'an tsaro da suka mara wa wakilin Gwamnan jihar Kebbi baya sun hada DCP.  J.A Amadi wakilin Kwamishinan Yansanda na jihar Kebbi, wakilin Darakta na SSS jihar Kebbi, Ag. C.O na Bataliya ta 1 na rundunar Soji Dukku Barracks Capt. Aliyu, Kwamandan rundunar tsaro na NSCDC na jihar Kebbi Hafiz Ringim, mai bayar da shawara ga Gwamnan jihar Kebbi ta fannen tsaro Janar Isah Dan Hanne mai murabus, Sakataren dindindim kan harkokin  tsaro na Caninet Office Birnin kebbi Alh. Bala Achale, tare da sauran manyan mutane da ke ruwa da tsaki akan lamarin.

Daga bisani Yombe ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Marigayi Muhammadu Mai Gadi wanda aka kashe tare da bayar da sadaka.Haka zalika, ya kai ziyara ga wadanda aka harba a Asibitin garin Illo inda suke jinyar raunukan harsashi.


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN