• Labaran yau

  Masarautar Argungu : An nada Sarakunan gargajiya 10 a Bachaka (Hotuna)

  A yau Lahadi 10/12/2017 ne aka yi nade-naden Sarautar Gargajiya a garin Bachaka na jihar Kebbi wanda ya sami halarcin wakilin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu wanda Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya wakilta kuma Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Kebbi ya halarta tare da sauran manyan baki daga ciki da wajen Masarautar Argungu.

  A nashi jawabin wakilin Mai Martaba Sarkin Argungu watau Sarkin Kabbin Argungu Alh. Ibrahim Hassan ya gode wa wakilin Gwamnan jihar Kebbi watau Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi da ya sami halartar wannan bikin nadin ya kuma kara da cewa Sarkin Argungu ya bukaci jama'a su ba shugabanni goyon baya a kowane mataki na shugabanci da suka hada da shugabanni na Gwamnati da na Sarauta, ya kuma ce "wannan shi ne zai ba mu dama mu ci gajiyar ayyuka na ci gaba da ake gudanarwa a mataki na Gwamnatin jiha da karamar hukuma"

  "Idan babu wannan da'a da biyayya abubuwa ba za su ci gaba ba. Muna mika godiya ga Gwamnatin Sanata Atiku Bagudu akan ayyuka da ake gudanarwa domin ci gaban al'umma. tare da yin kira a fadada ayyukan domin kowa ya samu.Ya kuma yi kira ga wadanda aka nada da su kasance masu yin ababe na ci gaba a wannan yankin nasu ".

  Wadanda aka nada a bikin nadin sun hada da :

  1. Alh. Muhammed Lawal Shehu - Wazirin Arewan Gabas na Bachaka
  2. Alh. Muhammed A. Daura - Turakin Arewan Gabas na Bachaka
  3. Alh. Bashar Shafi'u Bachaka - Dan Wakilin Arewan Gabas na Bachaka
  4. Alh. Ibrahim Bizo S.Kelle - Sarkin Zabarmawan Arewan Gabas na Bachaka
  5. Alh. Sani Abubakar Bachaka - Mataawallen Arewa Gabas Bachaka
  6. Alh. Umaru Gwamna Bachaka - Sarkin Yakin Arewa Bachaka
  7. Alh. Aliyu Ahmed Turba - Magajin Rafin Arewa
  8. Alh. Sani Musa Sangela - Tambarin Arewan Gabaas
  9. Alh. Abdullahi Koshe Danyaku - Talban Arewan Gabas Bachaka
  10. Alh Bako Kwankware - Sarkin Dorin Arewa.

  Makada da Mawaka sun nishadantar da bikin yayin da 'yan Tauri suka kara kayatar da bikin da nasu kwarewar.

  Daga bisani Mataimakin Gawamna Alh. Saila Yombe ya wakilci Gwamnan jihar kebbi Sanata Atiku Bagudu tare da Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Kebbi wajen ta'aziyyar Malam Isah  Abdullahi wanda ya rasu yana da shekara 50,ya bar Mata biyu da 'ya'ya. Marigayin kani ne ga Sakataren jam'iyar APC mai mulki na karamar hukumar Arewa.

  Daga Isyaku Garba

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Masarautar Argungu : An nada Sarakunan gargajiya 10 a Bachaka (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });