Rundunar 'yan sandan jihar Kogi da ke Najeriya ta ce ta kori jami'anta uku da take zargi da laifin fatauncin wiwi.
Ya kara da cewa hukumar NDLEA ce za ta gurfanar da su a gaban kotu
A cewar ASP Aya, rundunar 'yan sanda ba za ta lamunci duk wani jami'inta da zai bata mata suna ba.
Ana zargin 'yan sandan kasar da yin kaurin suna wajen aikata laifukan da suka kamata su hana aikatawa, ko da yake sun sha musanta zargin.
An gurfanar da matan da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda da mahaifiyarta da kuma 'yan uwanta a gaban kotu.
Sai dai Maryam ta musanta tuhumar.Har ila yau an tuhumi mahafiyarta, Maimuna Aliyu da 'yan uwanta Aliyu Sanda da Sadiya Aminu da laifin goge hujjar kisan kai domin kubutar da Maryam Sanda daga fuskantar da shari'a kan laifin kisan kai.
'Yan uwan Maryam din dai sun musanta tuhumar da aka yi masu.
Da aka fara gurfanar da Maryam dai, lauyan rundunar 'yan sandan birnin tarayyar Najeriya, Abuja, James Idachaba, ya nemi kotun ta ba shi lokacin domin ya gyara tuhumar da ake yi wa wadda ake zargin bisa sabbin bayanai da rundunar 'yan sandan birnin ta samu.
Yayin zaman kotun na ranar 7 ga watan Disamba domin jin sabuwar tuhumar, sai lauya James ya ce bai samu ya bai wa sauran wadanda ake tuhuma da aikata laifi kan lamarin sammaci ba.
Saboda haka sai kotun ta ba shi mako daya domin ya gabatar da sauran wadanda ake zargi da aikata laifi a lamarin.
Tsohon Shugaban kasa Yakubu Gowon, ya yi da-na-sanin rashin maida Jos a matsayin babban birnin tarayyar Nijeriya.
Gowon, ya ce ya ki
aiwatar da haka ne, don kada a ce ya cika tsananin nuna son yankin sa ko
kuma yi wa sauran yankunan Nijeriya mugunta.
Tsohon shugaban
kasar, ya bayyana haka ne a wurin bikin cika shekaru 26 da maida babban
birnin tarayyar Nijeriya daga Lagos zuwa Abuja.
Ya ce saboda ya na kallon garin Jos ya yi kusa da mahaifar sa, shi ya sa bai maida shi ya zama birnin tarayya Nijeriya ba.
Gowon ya nuna
takaicin sa a kan cewa, duk da shi ne ya fara nuna Abuja ce ta fi dacewa
ta zama birnin tarayya, amma ba a sanya wa wani titi ko gini sunan sa
ba, har sai da ya yi wa tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida
korafi.
Shugaban Majalisar
Dattawa Sanata Bukola Saraki, ya maida martani game da umurnin kotun
daukaka kara na maida shi kotun da’ar ma’aikata domin fuskantar
tuhume-tuhume 3 da su ka shafi karya wajen bayyana kadarorin sa.
A baya dai Kotun da’ar
ma’aikata ta wanke Bukola Saraki, bisa zargin sa da aikata laifuffuka
18, da su ka hada da karbar albashi fiye da daya, da mallakar dukiyar da
tafi karfin albashin sa, da rashin bayyana wasu kadadori da hannun jari
da ya mallaka, da kuma mallakar asusun ajiya a kasashen waje da sauran
su.
Mai magana da yawun
Sanata Bukola Saraki Yusuf Olaniyonu, ya ce tun da kotun daukaka karar
ta yi watsi da zarge-zarge 15 cikin 18, ya na da yakinin cewa sauran
ukun ma za a yi watsi da su, domin a cewar sa, Saraki bai aikata
wadannan laifuffuka ba.
Olaniyonu ya kara da
cewa, lauyoyin Saraki su na jiran cikakken bayani daga kotu, bayan sun
duba a tsanake za su dauki matakin da ya dace.
Majalisar wakillai ta
kafa kwamitin da zai binciki kamfanin NNPC bisa da zargin kin zuba
kudaden da su ka kai akalla Naira Biliyan 50 a cikin asusun bai-daya na
gwamnatin tarayya watau TSA.
Sai dai ‘yan
kwamitin sun bayyana cewa, maimakon kamfanin NNPC ya zuba kudaden inda
aka umurce shi, sai su ka karkatar da su zuwa bankunan ‘yan kasuwa.
Zargin dai ya fito
ne ta bakin shugaban kwamitin binciken, kuma dan majalisar wakilai daga
jihar Kano Alhaji Abubakar Nuhu Danburam, yayin da ya ke zantawa da
manema labarai.
Sai dai jami’an
kamfanin NNPC cewa su ka yi, sun yi hakan ne da sanin shugaba Muhammadu
Bahari, inda shi ma babban bankin Nijeriya ya gasgata hakan.