Labarai a yau Talata 26/12/2017

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakile wani hari da 'yan kungiyar BokoHaram su ka yi yunkurin kai wa a birnin Maiduguri a ranar Kirsimeti. 

Kwamandan rundunar sojojin ta Lafiya Dole a yankin arewa maso gabashin kasar Major Janar Nicholas Rogers shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa.

Ya ce dakarun sojin sun yi bata kashi da masu tayar da kayar bayan da suka farma wani wurin binciken ababen hawa na sojoji da ke wajen birnin a cikin motocin a kori kura

Janar Nicholas Rogers ya ce an kwashe sama da awa guda ana artabu tsakanin mayakan da sojoji.
Sanarwar ta ce babu asarar rayuka sai dai a lokacin da maharan ke tserewa sun kona wasu motoci biyu da wasu gidaje da ke kusa.

Hukumomi a birnin Maiduguri sun ce an kara tsaurara matakan tsaro a lokacin bukukuwan Kirsimeti.


Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Muhammad, wacce aka fi sani da Hadizan Saima ta ce masu yin fina-finan na Hausa sun zama abin nan da Hausawa ke cewa dankali sha kushe.

"Allah yana kallon abin da muke yi; idan muna yi don mu bata ko mu gyara mu fadakar, Allah ya sani.


"A cikin fina-finan da muke yi ana yin karatun Al-Qur'ani, ana jan baki a fassara, ana ce wa 'Allah ya ce, Annabi ya ce'. Shi ma duk wannan koya rashin tarbiyya ne?", in ji Hadiza, lokacin da take amsa tambayar da BBC ta yi mata kan zargin bata tarbiya da ake yi wa 'yan fim.

Ta kara da cewa: "Ka san mu dankali ne sha kushe, ana sonmu ana kushe mu. Amma haka za mu yi ta tafiya tun da haka Allah ya yo mu.

"Haka za a yi ta hakuri da mu, mu ma muna hakuri da masu kushe mu kuma a hankali za su fahimce mu. Na san wasu ma sun fahimta yanzu."

Jarumar, wacce akasari ta fi fitowa a matsayin uwa, ta kara da cewa ta soma sha'awar fina-finai ne tun lokacin da take da aure.

Sakamakon wani tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane uku baya ga dukiyoyin miliyoyin nairori da aka salwantar sanadiyyar kone-konen da ya biyo baya a Karamar Hukumar Bwari, Ministan Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, Muhammad Musa Bello, ya sanar da kafa dokar hana fita a fadin Karamar Hukumar daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na asuba agogon Najeriya.

Bayan da Ministan na Birnin Tarayyar Najeriya ya yi shelar kafa dokar hana fita din, sai mai magana da yawun Ministan, Abubakar Sani, ya gaya ma Hassan Maina Kaina, wakilin Sashin Hausa Na Muryar Amurka cewa fada ne ya gaure tsakanin wasu matasa, wanda ya kai ga daba ma dayan wuka. Ya ce daga nan ne fa gari ya yamutse har tashin hankalin da ya biyo baya ya kai ga kone-konen kaddarori ciki har da babbar kasuwar Bwari.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan Binrin Tarayya, Abuja ASP Anjuguri Manzah ya tabbatar da aukuwar lamarin. Amma ya ce an shawo kan lamarin. Manzah ya ce za a kaddamar da bincike saboda a gano musabbabin tashin hankalin a kuma hukunta duk mai laifi.Saurari shirin >>>


Fitaccen dan wasan Hausa, Adam A. Zango ya ce mutane su daina masa gyaran turanci domin ba yaransa bane.
 
Adam Zango ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa, inda yake cewa “Me ya sa mutane suke auna fahimtata da Turanci? Shin na taba fada ma wani cewa na je makaranta ne? ko turancin da nake yi ma a titi na koya.

Zango ya kara da cewa shi bai iya turanci domin shi dan fim din Hausa ne, “Ina yin fim di Hausa ne, kuma ina waka ne da harshen Hausa. Turancin da nake yi ma kawai ina yi domin masoya na da ba sa jin Hausa. Abin da na sani kawai shi ne na samu nasara a rayuwa,” in ji Zango.


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci ‘ya’yansa su dage su yi karatu, domin ba zai saci dukiyar Najeriya ba.

A wani shiri na musamman a kan Buhari, wanda Gidan Talabijin na Kasa wato NTA ta gabatar, Buhari ya ce yadda mutane ke kaunarsa ne ya sa yake siyasa. Sannan ya ce burinsa shi ne ya yi mulki mai kyau da aminci.

“Ina yin sallah sau biyar a rana domin in gode wa Allah da Ya sa mutane suke kaunata. Wannan abin murna ne yadda talakawa suke kaunata. Babban burina shi ne in yi shugabanci mai kyau da aminci a fili ba boye-boye."  

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN