• Labaran yau

  Labarai a yau Lahadi 17/12/2017

  Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar cika shekara 75 a duniya, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook.

  A ranar Lahadi ne shugaban zai cika shekara 75 da haihuwa.

  Mista Jonathan ya yaba wa shugaban inda yake cewa: "tarihi ba zai taba mantawa da jajircewarsa da kuma kokarin da yake wajen samar wa kasar nan kyakkyawar makoma ba."

  Daga nan sai ya ce yana taya 'yan uwa da abokan arzikin shugaban murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

  A watan Maris din shekarar 2015 ne Muhammadu Buhari ya lashe babban zaben kasar, bayan samun nasara a kan babban abokin hamayyasa Mista Goodluck Jonathan wanda ke kan karagar mulki a lokacin.

  Ma’aikatan Mai a Najeriya na barazanar shiga yajin aikin sai baba ta gani daga gobe Litinin, bayan cijewar tattaunawar da aka yi da kamfanin Neconde Energy Limited kan zargin na cewa an sallami wasu ma’aikata ba bisa ka’ida ba.

  Kungiyar ma’aikatan Man Fetur da aka fi sani da PENGASSAN, tace ma’aikatan zasu fara barin guraren aikinsu tun daga ranar Litinin da tsakar dare agogon Najeriya, bayan ta kammala taron jiga-jigan kungiyar. Ta kuma ce ma’aikata a fadin kasar suna jirane su fara yajin aikin.

  Kungiyar Ma’aikatan dai ta kara da kamfanin Mai na Neconde Energy Limited, kan abin da kira korar mambobinta ba bisa ka’ida ba.

  Dama Najeriya na fama da matsalar tashin farashi da kuma wahalar Mai biyo bayan barazanar tafiya yajin aiki da ‘yan kungiyar dillalan Man Fetur masu zaman kansu IPMAN suka yi.

  A sanadiyar mummunan karancin man fetur da gidajen mai da ke cikin garin Jos da kewaye ke fuskanta, cuwa-cuwar man ta haddasa mutuwar mutane biyu da konewar motocin tankuna uku cike da man fetur kurmusa da lalata wadansu guda biyu cike da man.

  Binciken da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta yi ya nuna ma na cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10:44 na daren Asabar din nan a lokacin da dillalan man su ke kokarin juye man da motoci biyar din su ka kawo daga Lagos da nufin saukewa a gidan man Echemmas da ke kan titin hanyar Bauchi a garin na Jos, amma sai su ka yi kokarin juye man a wata motar, don karkatar da shi, kamar yadda a ka yi zargi.

  To, amma nan take sai moticin su ka kama da wuta har tankuna ukun da ke dauke da man da wadansu kanana guda biyar da a ka ajiye su a gidan man su ka kone kurmus.

  Lamarin ya kuma haddasa mutuwar yaron mota daya, maigadin gidan man kuma ya jikkata tare da daya daga cikin dirobobin tankunan.

  Binciken da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta yi ya kara nuna ma na cewa, bisa namijin kokarin da hukumar kashe gobara ta jihar ta yi ne ya taimaka sauran tankunan mai guda ukun konewa kurmus kawai.

  Da ya ke managa da wakilinmu, daya daga cikin jami’an kashe gobarar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, babbar matsalar da su ka fuskanta ita ce ta rashin ruwa kusa da inda a ka yi gobarar, ya ce, idan ruwa ya kare mu su sai sun yi tafiyar kilo mita shida kafin su sami ruwa su cika tankunansu.

  A daidai lokacin da zabe 2019 ke karatowa, kungiyar GODD-NEWS NIGERA ta bayyana cewar Nijeriya ba da bukatar shuwagabanin da za su iya hada kan Nijeriya gami da shawo kan rikice-rikice ne a hanzu, kungiyar ta bayyana cewar tuni ta zakulo wani jigon da zai fidda Nijeriya daga halin-ni-‘yasu. Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar manema labaru da suka aiko wa gidan jaridar nan dauke da sanya hanun Ko’idinetan kungiyar Engr. Dauda J. Mbaya.

  Sanarwar ta ce “Manufa ta gari da kuma kyakyawar manufa shi ne Nijeriya ke bukatuwa da salon shugaban a irin wannan lokacin. Don haka, kungiyar GOOD-NEWS NIGERIA ta fito domin mara wa mutumin da zai wanzar da gaskiya, adalci da kuma hada kan ‘yan Nijeriya gami da wanzar da zaman lafiya a Arewa, Yammaci, Kudanci, da Gabas domin Nijeriya ta kasance dinkakkiyar kasa mai cikakken zaman lafiya”. In ji sanarwar Karanta saura >>

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

  Hoto: leadershipayau
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Labarai a yau Lahadi 17/12/2017 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });