• Labaran yau

  Ba'a taba hana ni shiga Amurka ba, Buhari ya mayar wa Atiku martani

  Wani hadimin shigaba Muhammadu Buhari watau Femi Adesina ya mayar wa tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar da martani sakamakon wani zargi da ya yi a wata tattaunawa da ya yi da wata jarida The Boss Newspaper inda Atiku ya bayyana cewa an taba hana shugaba Buhari shiga kasar Amurka.

  Dan jarida Dele Momodu ya tambayi Atiku kan jita-jitar da ake cewa an taba hana shi shiga kasar Amurka. Sai dai Alhaji Atiku ya musanta hakan kamar yadda BBC ta ruwaito..

  Daga nan ne sai tsohon mataimakin shugaban ya ce: "An taba hana Shugaba Buhari shiga kasar Amurka har na kusan tsawon shekara 15 saboda dalilin da suke da alaka da addini."

  Har ila yau Atiku Abubakar ya soki gwamnati Buhari kan yadda a cewarsa ta gaza cire wa 'yan Najeriya kitse a wuta.

  A watan jiya ne tsohon shugaban ya fice daga jam'iyyar APC. Abin da wadansu suke ganin shirye-shirye yake na kara tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2019.

  Sai dai bai fito ya bayyana hakan ba tukuna. Hakazalika shi ma Shugaba Buhari bai bayyana anniyarsa ta sake tsayawa takarar ba, kodayake a makon jiya akwai alamomin da suka fara nuna alamar hakan.

  **************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ba'a taba hana ni shiga Amurka ba, Buhari ya mayar wa Atiku martani Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });