B-kebbi: Karanta abin da Yombe ya ce a wajen taron kungiyar kanikawa NATA

Isyaki Garba |

An gudanar da taron kungiyar kanikawa ta Najeria reshen jihar Kebbi ranar Asabar, a tsohon tashar motar garin Birnin kebbi wanda ya sami halarcin wakilin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Banguda wanda Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya wakilta.

Taron ya sami walikcin shugabannin ressan kungiyar na kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a kungiyar reshen jihar Kebbi.

An tattauna ababen da suka ci wa kungiyar tuwo a kwarya wanda suka hada da yawan sace sace da ake yi masu a guraren sana'arsu da kuma bukatar sama masu matsuguni na dindindim watau Mechanic Village, daga bisani aka mika wa mataimakin Gwamna mukamin Uban kungiyar NATA na jihar Kebbi..

Wadannan bayanai sun fito daga bakin Eng. Muhammad Sani Chairman na sashen kungiyar na karamar hukumar Birnin kebbi da Eng. IBB chairman Dan Masanin NATA jihar Kebbi.Muhammed Sani ya ce kungiyar NATA tana horar da akalla masu yi wa kasa hidima guda 20 a kowane shekara wadanda ke zuwa wajen su domin su kara kwarewa akan karatun da suka yi a fannen ilimi irin nasu sakamakon turu su jihar Kebbi .

A nashi jawabi,wakilin Gwamnan jihar Kebbi a wajen wannan taron watau Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya fara da yi wa Allah godiya da ya basu damar halartar taron tare da mika godiyar Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ga kungiyar kanikawa ta kasa rashen jihar Kebbi.

Ya kuma tabbatar masu da cewa zai gabatar da korafe-korafensu ga Gwamnan jihar Kebbi tare da yi masu alkawarin cewa Mai girma Gwamnan jihar Kebbi zai share masu hawaye da yardar Allah. Ya yi bayani akan cewa za a sama wa kungiyar mota wadda za su kera da kansu domin su nuna hazakarsu akan baiwara da Allah ya yi masu.

Yombe ya kara da cewa kanikawa su ji tsoron Allah akan ayyukansu, kuma matukar an kira Sallah yana da kyau a ajiye aiki domin a je ayi Sallah domin shi ne kan gaba.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN