• Labaran yau

  'Yansanda sun haddasa hatsari bayan suna kwankwadan barasa suna tukin mota (Hotuna)

  Wasu 'yansanda sun haddasa hatsarin mota a hanyar Oron na cikin garin Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.Ana zargin cewa 'yan sandan suna tuki ne kuma suna kwankwadan barasa yayin da suka afka wa wata motar Bus na Stanford Microfinance Bank da ke dauke da fasinja.

  Yansandan da bayanai suka nuna cewa sun yi tatil da barasa sun saba wa dokar hanya bayan sun fito daga rukunin gidaje na Ewet lamari da ya haddasa raunata mutum 10 nan take.

  Kasancewar Kakakin Majalisar Dokoki na jihar Akwa Ibom Rt. Hon. Barr. Onofiok Luke a kusa da inda hatsarin ya faru ya sa nan take ya bukaci a kai wadanda suka raunata na wani Asibiti Premier Medical Center Edet Akpan Avenue ,Uyo inda ake yi masu magani.
  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: 'Yansanda sun haddasa hatsari bayan suna kwankwadan barasa suna tukin mota (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama