• Labaran yau

  Yadda Larabawa ke bautar da bakaken fata a Libya (Hotuna)

  An gano wata kasuwa a kasar Libya inda ake sayar da mutane 'yan asalin 'kasashen Afrika babaken fata a matsayin bayi bayan sun yi kokarin ketarawa zuwa kasashen turai ta kasar Libya sai a kama su a sayar da su ga 'yan tawaye wadanda daga bisani suka bautar da su kuma su azabtar da su.

  A wani bincike da gidan talabijin na CNN ya gudanr a makon da ya gabata akan lamarin a kasar Libya, sakamakon binciken ya nuna cewa yawancin 'yan kasashen Africa sukan karasa ta hanyar fadawa hannun 'yan tawaye a kasar Libya wadanda daga bisani suke sayar da su ga masu bukatar bayi wasu kuma akan cire wasu sassan jikin su ne kamar koda, anta ko zuciya domin fataucin su, lamari da ke haddasa mutuwar 'yan African da suka fada hannu.

  CNN ta ce da yawa daga cikin wadanda suka fada hannu akan yi masu fyade, kuma a kowane wata akan yi gwanjon 'yan Afrika bakaken fata ga Larabawa wadanda suke bukatar bayi a kalla sau biyu.Kimanin mutum 700.000 ne aka kiyasta sun fada hannun masu fataucin bayi 'yan Afrika a kasar ta Libya. Yanzu dai haka mahukunta a kasar ta Libya sun kaddamar da bincike akan lamarin
  Yadda aka gasa 'dan Najeriya da ran shi bayan an daure shi a karfen lantarki a kasar Libya

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Yadda Larabawa ke bautar da bakaken fata a Libya (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama