• Labaran yau

  Yadda Bachama suka kashe Fulani 45 a Numan na jihar Adamawa (Hotuna)

  An kashe akalla mutum 45 a wani hari da aka kai kan kauyukan Fulani a karamar hukumar Numan na jihar Adamawa wanda ake zargin 'yan kabilar Bachama da kitsawa ranar Litinin.

  Wasu Fulani da suka tsere domin su ceci rayuwarsu sun ce wasu 'yan kabilar Bachama da suke rera wakar yaki su kimanin 150 rike da mugan makamai sun shiga mazaunin Fulanin inda suka aikata kashe-kashe da kone-kone kan dukiyar Fulanin a kauyukan Shafaran, Shawal, Gumara, Kikam da Kadamti wadanda kauyuka ne a karamar hukumar Numan.
  Mubi: Tashin bom a masallaci ya kashe mutum 50 lokacin sallar asuba
  Bayanai sun nuna cewa maharan sun shigo kauyukan ne yayin da yawancin maza suka tafi wajen bukukuwan daurin aure aka bar Mata da yara wanda Maharan suka afka masu, suka yi masu mumunar kisan gillaiki ta hanyar sara da adda ciki har da yara da ake goyo su ma an sassare su da adda.
  Kalli Masallacin da tashin bom ya kashe mutum 50 a Mubi (Hotuna)
  A wani rahotu da wani 'dan jarida Ibrahim Abdulazeez ya ruwaito ya nuna cewa kakakin hukumar 'yansanda na jihar Adamawa  Othman Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma kara da cewa hukumar ta kaddamar da bincike akan lamarin domin a zakulo tare da kama wadanda suka aikata wannan aikin.   Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda Bachama suka kashe Fulani 45 a Numan na jihar Adamawa (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });