• Labaran yau

  Wasu barayi a karamar hukumar Shanga sun tuba daga yin sata (Hotuna)

  Yayin da lamarin sata da kuma fashi da makami ya zama ruwan dare a ko in cikin Najeriya, wani matashi ya tuba daga harkar sata har abada, tubar tasa wadda ya yi hadi da rantsuwa ya ce har abada shi kam ya daina sata.

  Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai da Mai ba Gwamnan jihar Kebbi shawara ta fuskar tsaro Gen. Isah Dan Hanne tare da Uban kasar Maginga Alh. Nuhu Abdulmalik da sauran manyan baki suka shaida rantsuwar barin satar a fadar Uban kasar Maginga.

  wasu Fulani da suka  shaida rantsuwar tuba daga sata
  Shirin wanda Gwamnatin jiha karkashin shugabancin Sanata Atiku Abubakar Bagudu ta yi na'am da shi , Gen. Dan Hanne ya jagoranci shirin zakulo tare da bukatar barayi a ko ina suke a cikin jihar Kebbi su zo su tuba domin Gwamnati ta taimaka masu da tallafi su ma su zama nagartattun mutane a cikin al'umma.

  Tsohon barawon da aka rantsar ranar Assabar mai suna Muhammadu Yelle daga garin Shangil ya tuba har abada tare da karin wadansu barayin a yanayi na gabatar da rantsuwa da Mal. Muhammadu Jammare Farfara ya gudanar.Bayanai sun nuna cewa fiye da mutum 16.000 ne suka tuba daga yin sata a jihar Kebbi karkashin wannan shirin.
  Gen. Dan Hanne (Murabus)

  Barawon ya daga Alqur'ani ya dora a kan sa hannu buyu ya kuma yi rantsuwa har sau uku cewa ba zai sake yin sata ba ,ko ya ba wani barawo bayani, ko a shirya da shi ayi sata, ko ya ajiye kayan sata, da dai sauran su.
  Alh. Samaila Yombe tare da Uban kasan Maginga Alh. Nuhu Abdulmalik

  A nashi jawabi Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh.Samaila Yombe Dabai ya yi Allah wadai da halin wasu Fulani wadanda ke sata, Yombe ya kara da cewa abun kunya ne a ce yau Fulani ne ake rantsarwa wai ya bar sata. Ya kara da cewa sata baya cikin gadon Fulani saboda haka duk wani Bafullace da ke sata don Allah ya daina.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wasu barayi a karamar hukumar Shanga sun tuba daga yin sata (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });