Suru: Rikicin manoma da makiyaya ya yi sanadin salwantar dukiya

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya kai ziya a tungar Bakoshi da ke karamar hukumar Suru sakamakon wani tashin hankali da yayi sanadin salwantar  dukiya da kayan amfanin gona da dama.

Tawagar ta Gwamna tana tare da Kwamishinan 'yansanda na jihar Kebbi  Kabiru Ibrahim ,Daraktan SSS na jihar Kebbi Muhammad Kaumi da Kwamandan NSCDC, Hammani Ringim.

Bayanai sun nuna cewa rigimar ya samo asali ne bayan an gano gawar wani manomi 'dan shekara 30 kusa da tungar Fulani sakamakon haka ya sa wasu manoma suka kona tungar tare da kashe dabbobi da dama.

Gwamna Atiku Bagudu ya yi wa wadanda lamarin ya rutsa da su ta'a ziyya tare da gargadi ga jama'a kan cewa nan gaba Gwamnati ba za ta lamunci daukan doka a hannu ba kuma duk wanda ya sake aikata irin wannan laifin zai hadu da fushin hukuma.

Haka zalika Gwamnan yayi bayani cewa sakamakon bincike na Likitoci daga Asibiti ya nuna cewa Manomin yayi mutuwar Allah ne ,watau lokaci ne ya yi ba wai an kashe shi bane.

Daga bisani Gwamna Bagudu ya bayar da tufafi da kayan abinci ga wadanda lamarin ya rutsa da su.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN