• Labaran yau

  SSS ta gabatar da Sambo Dasuki a gaban Kotu (Hotuna)

  Hukumar tsaro ta SSS ta gabatar da Sambo Dasuki a gaban wata babban Kutun tarayya a birnin Abuja ranar Alhamis bisa shara'ar da ake yi wa Olisa Metuh akan zargin cin hanci da rashawa ta hanyar karbar N400m daga hannun Sambo Dasuki.

  Sambo Dasuki wanda tsohon mai ba shugaban kasa shawara ne ta fuskar tsaro ya fada cikin rikita -rikitan kudade ne bayan an zargi ofishinsa da almubazzarantar da kudaden jama'a kafin zaben shugaban kasa a 2015.

  Hukumar SSS tana tsare da Dasuki kusan shekara daya saboda abinda ta kira dalilan tsaro.


   Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: SSS ta gabatar da Sambo Dasuki a gaban Kotu (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama