Ranar 'yan jarida na Duniya ,sakon taya murna - Isyaku Garba

ISYAKU.COM na taya 'yan jaridar jihar Kebbi,Najeriya da Duniya gaba daya murnar ranar 'yan jarida na Duniya Litinin 6 ga watan Nuwamba 2017.Haka zalika muna yi maku fatan alhairi tare da rokon Allah ya kare kowane 'dan jarida a ko'ina yake a Duniya.

Muna son mu yi amfani da wannan dama mu mika godiyar mu ga BBC ACADEMY watau makarantar koyon aikin jarida na BBC,Alison Courses, da sauran cibiyoyi da muka sami horo domin sanin makaman aiki daga gurinsu.

Ina son in yi amfani da wannan dama domin in yi kira ga jama'a musamman 'yan Social Media cewa a daina gabatar da kai a matsayin 'dan jarida.Aikin jarida yana da ka'idodi wanda na farkon ginshiki shine karatun aikin jaridar a mataki na farko sai samun kwarewa na aikatau.

Sau da yawa 'yan Social Media kan gabatar da kansu a matsayin 'yan jarida wanda bai dace ba.Marmakin a gabatar da kai a matsayin 'dan jarida alhalin 'dan Social Media ne sai ayi amfani da kalmar 'DAN RAHOTU NA SOCIAL MEDIA amma ba wai 'DAN JARIDA  ba.

Duk 'dan Social Media da yake son ya zama 'dan jarida yana da kyau ya je ya karanci yadda ake aikin jarida  kuma aikwai makarantu da cibiyoyi da za ka iya yin karatun ta yanar gizo daga gida.

Ga masu korafi akan cewa labaran mu na tashin hankali ne, amsar mu a nan ita ce ba haka zancen yake ba. Kafin mu fara wallafa labarai mun dauki wata uku muna bibiyan irin labarai da al'umar Hausa ke bukata wanda muka tattaro daga BBC, RFI, VOAHAUSA, DW HAUSA, AMINIYA, LEADERSHIP HAUSA, PREMIUMTIMES HAUSA, NAIJ.COM da sauransu, sai muka gano cewa Bahaushe ya fi son a tsegunta masa labarin AL'AJABI, kuma bisa wannan sakamakon bincike ne muka dora tubalin labaran mu wanda mu ke daukan nauyin shafinmu da labaran da muke ruwaito maku.

Muna tabbatar maku cewa wadannan labarai an fi karanta su domin wasu kafafen labarai basu labarta irin wadannan labaran amma mu sai mu labarta maku domin nishadantarwa, fadakarwa da sanarwa.

Kofarmu a bude take domin samun huldar zumunci tare da ku ko gabatar mana da korafin ku masu ma'ana kuma za ku iya tuntubar mu kai tsaye a lamba na kasan wannan labari .

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN