Barka da zuwa Mujallar ISYAKU.COM

 • Labaran yau

  Mutum 50 sun mutu sakamakon harin 'yan bindiga a Zamfara

  Akalla mutum 50 ne aka kashe a wasu sabbin hare-hare da wasu 'yan bindiga suka kai a wasu kauyuka a jihar Zamfara a 'yan kwanakin baya wanda ya yi sanadin salwantar rayuka 50,hadi da wanda ya gudana ranar juma'a wanda a harin kadai maharan suka kashe akalla mutum 25 a wani kauye.

  Mazauna garin Faro da Kubi da Shinkafi a jihar sun ce, ana zaman dar-dar saboda wasu mahara sun shiga garin inda suka far wa mutane.

  Sama da mutum 50 ne mazauna garuruwan suka tabbatar da mutuwarsu a hare-hare mabambanta da aka kai kauyukan da mutane suka gudu dan tsira da rayukansu.

  Dakta Sulaiman Shu'aibu, shi ne sarkin shanun Shinkafi ya shaida wa BBC cewa, cikin daren Jumma'a ne mutanen da ake zargin suka je wani kauye mai suna Tunga Kabau, suka kashe mata ashirin da biyar da kuma maza tara kana kuma daga bisani suka bankawa kauyen wuta.

  Daga nan kuma sai suka nufi wani kauyen da ake cewa Mallabawa, nan ma suka kashe mutum goma sha tare.

  Dakta Sha'aibu ya ce, gaskiya yakamata gwamnati jihar Zamfara ta sake damara wajen kawo karshen hare-haren da masu satar shanu ke kai wa wasu kauyukansu.

  Su ma mazauna garin Faro da Kubi duk a jihar ta Zamfaran, sun ce kwana biyu sun dan samu sassaucin hare-haren 'yan ta'adda da barayin shanu, da kuma dauki dai-dai da ake musu.

  Amma kuma tun daga makon da ya gabata hare-haren sun sake dawowa.

  Wani mazaunin garin Faro ya shaida wa BBC, cewa barayin shanun sun yi mummunar barna da ta hada da asarar rayuka da kona amfanin gona.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutum 50 sun mutu sakamakon harin 'yan bindiga a Zamfara Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });