Mutum 250 sun mutu a Gombe da Plateau sakamakon rashin maganin cizon maciji

Rashin maganin dafin saran maciji ya haddasa mutuwar fiye da mutum 250 cikin mako uku da suka gabata a yankin jihar Gombe da Plateau .

An shaida wa wani dan jarida da ya ziyarci guraren bayar da maganin cizon maciji a  babban Asibitin Kaltungo, Ali Mega Pharmacy Gombe da Comprehensive Medical Centre Zamko na jihar Plateau cewa maganin dafin maciji ya kare.

Majiyar ta shaida masa cewa magungunan dafin cizon maciji kamar Echitab Plus ICP polyvalent da Echitab G monovalent sun kare tun mako na farko a watan Oktoba kuma ba'a kawo maganin ba tun watan Agusta.

Bayanai sun nuna cewa an fi samun yawan matsalar ta saran maciji a lokacin girbin amfanin gona.Yanzu haka guraren bayar da maganin saran maciji na Kaltungo kan yi amfani da maganin dafin maciji Indian-anti-Venom wanda a cewarsa bai da inganci sosai domin sau da yawa sukan bayar da kwaya 6 ga mutum bisa ga kwaya 1 na Echitab G wanda ke warkar da mai fama da matsalar nan take.

Yanzu haka guraren bayar da maganin saran maciji a wannan yankin suna cikin wani hali na rashin sanin alkiblar jinya ga masu fama da matsalar saran na maciji sakamakon karewar magani da ke haifar da macewar a kalla mutum 6 a kullum

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN