• Labaran yau

  Motar barayi ta kama da wuta ta kone bayan sun saci rago (Hotuna)


  Rana ta bace wa wasu barayi bayan sun saci rago a wani mayanka suka saka a motar su kirar BMW suka buda a guje da motar yayin da wasu mutane suka dafa masu baya da gudun gaske sai tayar BMW ta fashe barayin suka ki tsayawa, sakamakon tafiya da suka ci gaba da yi kuma wuta na baltsi daga gyaren motar sai motar ta kama da wuta.

  Bayan gobara ta rufe motar sai barayin suka fita suka ranta na kare da kafafun su ,suka bar rago a cikin motar da sauran kayanabinci doya da sauransu wanda suka kone rago kuma ya gasu.

  Kasancewa haka ne yasa wasu mazauna kusa da inda lamarin ya faru suka yi yasoson naman ragon da dama ya gasu kuma suka je suka cinye naman ragon.   Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Motar barayi ta kama da wuta ta kone bayan sun saci rago (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama