• Labaran yau

  Mi ya faru a Taron jam'iyar APC na Kudancin jihar Kebbi ? (Hotuna)

  Daga Isyaku Garba - Birnin Kebbi |

  An gudanar da wani babban taro na masu ruwa da tsaki a harkar jam'iyar APC yankin kudancin jihar Kebbi a garin Warrah na karamar hukumar Ngaski ranar Assabar 25 ga watan Nuwamba . Taron ya kasance fili da aka tattauna ababe da ke fuskantar al'ummar wannan yanki wanda ya hada Masarautar Zuru da Yauri.

  Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya fara da kai ziyarar ban girma a Fadar uban kasar Maginga Alh. Nuhu Abdulmalik Warrah ,basaraken ya yi godiya tare da tabbatar wa Yombe goyon bayan su ga Gwamnatin jihar Kebbi .

  Daga bisani tawagar Mataimakin Gwamnan ta zarce zuwa gidan tsohon Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Abubakar Musa Garkuwan Yauri, inda Mataimakin Gwamna ya yi gaisuwar sada zumunci da ban girma.


  Daga bisani Yombe ya ziyarci harabar Makarantar Sakandare na kimiyya a garin Warrah inda ya gaisa da dalibai da aka jera su domin karramawa ga Mataimakin Gwamnan wanda a 'dakin taro na Makarantar ne aka gudanar da babban taro da aka yi na jam'iyar ta APC kudancin jihar Kebbi.

  Bayan da aka buda taro da addu'a, an gabatar da korafe korafe da dama da ake ganin sun dabaibaye kananan hukumomi 7 da ke karkashin kudancin jihar Kebbi,  kadan daga ckin su har da rashin aikin yi ga matasa, hanyoyi, ruwansha, kiwon lafiya, samun karin wakilci ga Gwamnati da dai sauransu.

  Haka zalika an bukaci a sauwaka yanayi na samun katin zabe ga mutane yadda za su same shi cikin sauki bisa zargin cewa da dama daga cikin 'yan jam'iyar ta APC basu da katin zaben.Sai kuma zancen shirin taimaka wa matasa da N5000 da kuma shirin tallafi na Gwamnati wadda matasan suka ce sun ji shiru.

  Alh. Abubakar Abiola Zuru ya bukaci Gwamnati ta saki kudi ya zagaya jama'a domin a kara taimaka wa Gwamnati domin samun biyan bukata ga jama'a da kuma ita Gwamnati, Ladidi Labaran Yauri ta bukaci a taimaka wa mata musamman zawarawa da Mazajen su suka rasu suka bar su da Marayu.

  Bayan da aka gama sauraron korafe korafe, an ba jama'a amsa akan tambayoyi da korafe korafe da suka yi inda Hon. Sodangi Ngaski ya yi bayani akan kadan daga cikin ababe da suka aiwatar ta hanyar yin doka a majalisar dokoki na jihar Kebbi da ya bukaci Gwamnati ta hanzarta kammala dukan ayyukan da aka fara ,ya bayar da misalin hanyoyi kamar na Malado, Warrah , Danko wasagu da sauransu.Ya ce burin yan yankin kudancin jihar Kebbi ne su ga cewa Gwamnan jihar Kebbi a 2023 ya fito daga wannan yankin.

  Ya kara da cewa Gwamnatin jihar Kebbi tana kan gyara hanyoyin Utolo, Marabo, Saminaka, Shanga da Dibis.A nashi jawabi Hon. Abdulrahman Muhammed Manga ya bukaci a kara dankon zumunci a tsakanin Masarautun biyu na Zuru da Yauri, ya kuma bukaci kujerar Sanata a 2019 ya kasance a hannun Yauri amma kujerar Mataimakin Gwamna ya kasance a Zuru.

  Hon. Abdulrahman ya kara da cewa an gama da jam'iayar PDP a Masarautar Zuru sakamakon canja sheka da jiga jigan jam'iyar PDP na Zuru suka yi zuwa APC. Alh. Doya Zuru da Alh. Saidu 'dan Kolo da sauran tawagar su sun halarci taron APC na yau.


  Yayin da yake jawabi, Sakataren Gwamnatin jiha Alh Babale Umar , ya yi mamakin jin cewa kudi baya isa hannun jama'a ,kuma cewa ba'a yi ayyuka ba a wasu wurare a yankin yammacin jihar Kebbi.Alh. Babale ya daga wani File wanda yace yana dauke da duk wata kwangila da Gwamnatin jihar Kebbi ta bayar da sunayen 'yan kwangilan da ko nawa ne aka bayar. Ya musanta cewa Gwamnati bata bayar da kudi sai dai idan wakilan jama'a suna yi masu rowa ne.Ya kara da cewa zai bayar da kofi na abin da File din ya kumsa ga shugabannin kananan hukumomi da kwangilolin suka shafa domin su gani don a yi wa Gwamnati adalci.

  Babale ya ce a lokacin Gwamnatin Sa'idu Dakingari , Gwamnatin jihar Kebbi tana samun Biliyan 7 a kowane wata daga Gwamnatin tarayya, amma a yanzu Gwamnatin jihar Kebbi tana samun Biliyan 4 ne daga Gwamnatin tarayya wanda bayan an biya albashin ma'aikata abin da yake ragewa a hannun Gwamanati bai wuce N300m ba a wata.

  Daga karshe Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya fara da yi wa Allah godiya, sa'annan ya ce Allah ya yi wa jihar Kebbi gata domin ya ba jihar Kebbi shugaba Sanata Abubakar Atiku Bagudu , adali,shugaba na saurarawa domin shi ne ke gudanar da tafiyar Gwamnati na jihar Kebbi.Ya ce "korafe-korafe da aka samu na rashin yi, an yi, sai dai bayanai da babu su a da kuma yanzu an samu sakamakon adalcin shugaban mu Gwamna Atiku Bagudu da adalcin sa ya sa jiga-jigai da dubannin 'yan jam'iyar PDP suka canja sheka suka dawo tafiyar APC ta adalci karkashin Mai girma Gwamna Atiku Bagudu".

  Yombe ya ce Gwamnatin Sanata Atiku Bagudu ta cika alkawarin da ta yi wa jama'ar yankin a lokacin yakin neman zabe na 2015 wanda ya kunshi taimakawa a kan harkar noma, hanyoyi, inganta kiwon lafiya da sauransu.Ya bayar da misali da hanyar Ngaski zuwa Warrah wanda Gwamnatin jihar Kebbi ta gyara.Ya ce yanzu haka akwai matasa 75 daga kananan hukumomin Shanga da 80 daga Yauri wadanda ke fuskantar tantancewa domin shiga aikin Soja karkashin shugabancin Gwamna Atiku Bagudu da sauran karin misalai.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Mi ya faru a Taron jam'iyar APC na Kudancin jihar Kebbi ? (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama