• Labaran yau

  Matasa sun rantse da Qur'ani,suka fice daga kungiyar boko haram sakamakon yunwa (Hotuna)


  Wasu matasa 'yan kungiyar boko haram sun tuba kuma sun yi watsi da akidar kungiyar ta boko haram.Rahotanni da suka fito daga kasar Cameroon sun nuna cewa matasan sun mika kansu ne ga mahukunta domin rabin kansu.

  Majiyar tamu ta labarta mana cewa matasan wadda suka ce su dai sun gaji ne da fuskantar wahala, tashin hankali da kisan bayin Allah  da basu ji basu gani ba.Haka zalika matasan sun ce sun fuskanci matsanancin yunwa yayin da suke tare da kungiyar ta boko haram a yankin gabacin kasar Cameroon.

  Matasan sun rantse da Alkur'ani akan cewa ba zasu sake komawa cikin kungiyar ta boko haram ba.

  An sakaya sunan garin da lamarin ya faru saboda dalilan tsaro.   Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Matasa sun rantse da Qur'ani,suka fice daga kungiyar boko haram sakamakon yunwa (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama