• Labaran yau

  Matar 'dan Dr. Bello Haliru ta kashe mijin ta Bilyamin sakamakon kishi

  Akwai kwakkwarar zargi cewa matar 'dan tsohon shugaban PDP Dr. Bello Haliru watau Maryam Sanda ta kashe Maigidanta Bilyamin Muhammed Bello ta hanyar daba masa wuka har sau uku .

  Majiyar mu ta labarta mana cewa Maryam wadda diya ce ga Hajiya Maimuna Aliyu shugaban Aso Savings ta daba masa wuka sau uku daga bisani ta sake daba masa wuka a al'aurarsa daga kuma ta cije masa kunne kafin ta saka shi a cikin mota ta kai shi Asibiti daga bisani ya rasu.

  Bayanai sun nuna cewa takaddamar ta taso ne bayan Maryam ta ga wani sakon SMS a wayar Bilyamin kuma ta zarge shi da cin amanarta sakamakon haka ne ta aikata wannan aikin a gidansu da ke Maitama a birnin Abuja.

  Wata majiya ta labarta cewa tun lokacin da Maryam ta cije kunnen Bilyamin kuma aka yi masa magani a Asibiti, an shawarce shi akan cewa kada ya koma gida, amma sai ya koma gidan kafin Maryam ta aika shi lahira.

  Yanzu haka zancen na hannun sashen bincike na CIID da ke babban birnin tarayya Abuja inda suke gudanar da bincike.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Matar 'dan Dr. Bello Haliru ta kashe mijin ta Bilyamin sakamakon kishi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });