Barka da zuwa Mujallar ISYAKU.COM

 • Labaran yau

  Masarautar Zuru ku ci gaba da ba Gwamnatin Bagudu goyon baya - Samaila Yombe

  Daga Nura Bena, Isyaku Garba |

  Mai girma Mataimakin Gwamnan jihar kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya yi kira ga al'ummar Masarautar Zuru da su ci gaba da mara wa Gwamnatin jiha baya akan shirye shirye da manufofinta domin Kara samar wa jama'ar  yankin karin ayukkan ci gaba.

  Alh. Samaila yombe Dabai yayi wannan kiran ne a lokacin da yake lale marhaban da manyan 'Yan siyasa da masu hannu da tsaki a sha'anin siyasar yankin na masarautar ta Zuru da kewaye a ofishin sa. 

  Mataimakin Gwamnan yakara da cewa ya zama wajibi ya gode wa Maigirma Gwamna Sanata Abubakar Atiku Bagudu  (Matawallen Gwandu) akan irin kuwarsa ga ci gaban yankin tare da samar wa jama'ar yankin abubuwan more rayuwa hadi da walwalar al'umma.

  Ya ce ya nuna jagoranci nagari  a Karkashin jamiyyar APC chanji. Musamman idan a kayi la'akari da bada Mukaman SSA  watau masu  baiwa Gwamna shawara na musamman, da dai saurasu.
   
  Alh. Samailia  Yombe Dabai ya jadda da kudurin Gwamnatin jiha na kawo karin ababen more rayuwa ga al'ummar jihar nan da ma kasa baki daya


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Masarautar Zuru ku ci gaba da ba Gwamnatin Bagudu goyon baya - Samaila Yombe Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });