Ku yi rijistar kungiyoyin ku domin samun taimakon Gwamnati - Samaila Yombe

Daga Isyaku Garba - Birnin kebbi |

Kungiyar hadin kan kungiyoyi da taimaka wa jama'a domin koyon kananan sana'oi Kebbi state Co-operative Federation ta kai ziyarar bangirma da neman gudunmuwa, neman shawara tare da mika wuya ga gwamnatin jihar Kebbi ga Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai.

Tawagar wacce Hajiya Hadiza Hassan ta yi jawabi a madadin sauran manbobinta ta yi bayani akan nassarori da kungiyar ta samu wanda ya hada da gina dakin taro a kasar Zuru tare da samun na'urar shanya abinci wadda jami'ai suka sami hiro kan yadda ake tafiyar da aikisu.

Haka zalika kungiyar ta mika wa Mataimakin Gwamna Alh.Samaila Yombe darajar kasancewa "Baban kungiyar".

A nashi jawabi, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya fara da yi wa Allah godiya inda yace" Da farko dai nayi wan Allah godiya da ya bamu shugaba Sanata Abubakar Atiku Bagudu a matsayi Gwamnan jihar Kebbi wanda abin da ya sa a gaba shine tabbatar da sha'anin aikin gona da ya sa ya zama jagora ".

Yombe ya kara da cewa "aikin ku yana cikin tsarin wannan tafiya, sakamakon haka duka abin da kuka fada a nan zan je in gaya wa Mai girma Gwamnan Kebbi domin a san yadda za'ayi idan Allah yarda".

Mataimakin Gwamnan ya yi tsokaci akan cewa duk wani abin kirki ko na alhairi baya samuwa cikin sauki sai an sha wuya, amma yace daga karshe sai a ga wannan abu ya zama abin koyi da burgewa.

Ya kuma kara da cewa ana rijistan kungiyoyi , saboda haka a yi kokari a yi rijistan kungiyoyin su  domin su kasance cikin wadanda za'a taimaka wa. Yombe ya bukaci kungiyar ta rubuto bukatun ta domin gabatarwa ga Gwamnati.

Jagorar kungiyar a ziyarar ta mika wasu turare, man shafawa da sauran kayan kamshi da 'yayan kungiyar suka yi da hannun su ta hanyar horo da suka samu a kungiyar.

Daga cikin wadanda suka halarci ziyarar sun hada da Shugaban kungiyar Abdullahi Umar Jega , Ma'ajin kungiyar Haj. Hadiza Hassan, da mambobin kungiyar ,Hon. Abdullahi Sani, Haj. Maimuna Jega, Margret Bauta, Haj. Mary Yusuf, Haj. Mai Buruji Gwandu.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN