• Labaran yau

  Ko ka san dabbobi na yin Luwadi ? - Labarin wani Zaki 'dan Luwadi

  Daga Isyaku Garba |

  Lamarin dai da ban mamaki yadda aka kula da karuwar aikata luwadi a tsakanin dabbobi a Duniya shekaru da dama da suka gabata wadda wasu ke yi wa kallon lamari ne na al'adar rayuwa a tsakanin dabbobin.Wannan labarin wasu Zakuna ne guda biyu da wani mai taukan hoto daga London Paul Goldstein ya dauki hotunansu yayin da suke barbara da ya kaisu ga yin luwadi yanayi da ya ba mutane masu kallo mamaki a yankin Masai Mara na kasar Kenya.

  Dr Ezekiel Mutua wani babban jami'i ne a hukumar tantance fina-finai a kasar ta Kenya ya ta'allaka laifin akan 'yan luwadi da ke aikata luwadi a gaban dabbobin.Ya kuma bukaci a ware wadannan dabbobi har sai an yi bincike akan musabbabin da ya jawo dabbobin suke aikata luwadi.

  Su dai wadannan Zakunan sun fara sumbatar juna ,suka rungumi juna ,bayan sun yi wasar soyayya daga bisani suka yi jima'i wadda ya dauki akalla minti daya bisa ga tsawon lokaci da ya kamata na sakan 15 zuwa 20 idan Zaki yana saduwa da Zakanya.


  Sai dai wani sakamakon binciken kimiyya a karni na 20th ya nuna cewa harkar luwadi tsakanin dabbobi ko Zakuna sanannen lamari ne a kimiyance.Lissafin kimiyya ya nuna cewa kashi 8 na saduwa tsakanin Zakuna ko dabbobi yakan auku ne tsakanin na miji da na miji.

  Haka zalika masana kimiyyar rayuwar dabbobi sun tabbatar da faruwar harkar luwadi tsakanin dabbobin daban-daban har iri 450 a tsakanin jinsin dabbobi da wasu halittu a fadin Duniya.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Ko ka san dabbobi na yin Luwadi ? - Labarin wani Zaki 'dan Luwadi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama