Kalli wanda ya tone gawaki 7 ya yanke kanu a makabartar Musulmi

Dubun wani matsafi 'dan shekara 25 ya cika yayin da jami'an 'yansanda a jihar Kwara suka kama shi dauke da wani buhu wanda ke kunshe da kwarangwan kanun mutane guda bakwai akan hanyar  Ajase-Ipo a garin Ilorin.

Kawamishinan 'yansanda na jihar Kwara Lawan Ado ya ce wanda aka kama ya ce ya tone gawakin ne a wata Makabartar Musulmi a Igbo Owu na karamar hukumar Ifeledun a ranar Talata.

Kawamishina Lawal Ado ya ce rundunarsa za ta gurfanar da Matsafin a gaban Kotu da zarar ta kammala bincike.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN