• Labaran yau

  Kalli wadanda suka tone gawaki a makabarta suka yanke kawuna

  Jami'an 'yansanda a jihar Oyo sun kama wasu mutum uku dauke da kanun mutane, kafafu da sauran sassan jiki wanda suka tone daga wata Makabartar Musulmi a yankin Isele na garin Ogbomoso a cikin jihar Oyo.

  Vanguard ta ruwaito cewa wadanda aka kama sun hada da Alfa Babatunde Kareem dan shekara 37, Taofeek Bello dan shekara 22, da Adebayo Yusuf dan shekara 23.

  Taofeek ya ce wannan ne karon farko da ya yi kokarin yin amfani da sassan jikin bil'adama domin yin amfani da su wajen yin sihirin samun kudi.Ya kara da cewa "Da misalin karfe 8:00 na dare muka je Makabartar Isele muka tone wasu gawaki yayin da muke dawowa ne muka hadu da wasu yara wadanda suka bukaci su san abin da muka dauko tunda yana wari mai tsanani."

  "Amma sai muka tsere yaran sun kama Kareem wanda daga bisani ya zo da su gidajen mu aka kama mu."

  "Niyyar mu ita ce bayan mun samo wadannan sassan jikin bil'adama za mu kone su ne sai mu nika da sabulu na musamman sai mu yi wanka da safe da shi da dare kuma mu yi kunu da shi wanda bayan mun aikata haka aljanu za su kawo mana kudi da talatainin dare"

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli wadanda suka tone gawaki a makabarta suka yanke kawuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });