• Labaran yau

  Jami'an tsaro sun dakile hatsaniya da ya kai ga kone konen tayoyi a Kalgo

  Da ranar yau an sami hatsaniya da ya kai ga sa matasa su yi kone konen tayoyi a garin Kalgo hedikwatar karamar hukumar Kalgo a jihar Kebbi.Bayanai sun nuna cewa ana zargin cewa lamarin ya samo asali ne bayan wani ma'aikaci ya harzuka yayin da ya ga an saka N4000 a takardar biyan shi  albashi marmakin N17000 da ya saba karba wanda daga bisani ya kwace takardar biyan albashi watau Voucher ya fito da ita ya shaida wa jama'a lamari da ya sa sauran jama'a suka kwace voucher kuma suka yage takardar.

  Wata majiya ta shaida mana cewa tuni dai Ma'aikata suke ta kokawa sakamakon wani binciken sahihancin adadin Ma'aikata a karamar hukumar lamari da ya sa aka rage adadin albashin da wadansu ke karba. Masu hatsaniyar sun yi ta ihu suna cewa basa son shuganban karamar hukumar tasu.

  Masu hatsaniyar sun kona tayoyi akan magamar hanyar Bunza,Jega da Birnin kebbi yayin da suka kona wasu tayoyin a bakin babban kofar shiga Sakatariyar karamar hukumar ta Kalgo.

  Isowar Kwamishinan 'yansanda na jihar Kebbi cikin lokaci tare da tawagarsa ta jami'an tsaro da ya kumshi wakilin Darakta na SSS da kwamanda na NSCDC a wajen ya janyo dakile lamarin daga kazamcewa domin manyan jami'an tsaro sun yi na mijin kokari domin ba jama'a hakuri domin su koma gidajensu tare da yi masu alkawarin cewa doka za ta yi aikin ta wajen tabbatar da adalci domin ganin an zauna lafiya.

  Babu wani bangare na sakatariyar da aka kona haka zalika babu wani shago ko gida da lamarin ya shafa face wani bangare na harabar filin Sakatariyar da wutar ya shafi ciyawar da ya kama da wuta ya kone kafin motar jami'an kashe gobara ta iso wajen.

  Wata majiya ta shaida mana cewa ana kayautata zaton cewa za'a ci gaba da biyan ma'aikatan albashin su ranar Alhamis duk da faruwar wannan lamarin.

  **************************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jami'an tsaro sun dakile hatsaniya da ya kai ga kone konen tayoyi a Kalgo Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });