• Labaran yau

  Ibrahim Bagudu a Facebook 'dan rito ne ba shafi na ba ne - Kanin Gwamna Bagudu

  Wasu bayanai da muka samu sun nuna cewa wani mutum yana bata sunan kanin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu sakamakon buda wani shafi na sada zumunta a Facebook da wannan sojan gonar ya yi amfani da suna tare da hoton kanin Gwamna watau Alh. Ibrahim Bagudu.

  Bayanai sun nuna cewa wannan mutum yana yin rito da sunan kanin Gwamna har kuma wadanda yake yaudara suna ganin cewa kamar shafin Alh. Ibrahim ne.

  Amma gaskiyar lamarin shine Alh. Ibrahim Bagudu baya da shafi a Facebook, kuma baya wata harka ta mutunci da wani ta hanyar shafin Facebook amma sai dai ta fuskantar juna kai tsaye ido da ido.

  Sakamakon haka ake sanar da jama'a cewa babu hannun Ibrahim Bagudu a cikin wannan shafin na Facebook da ke dauke da sunan IBRAHIM BAGUDU wanda har wasu suna tura ababe masu muhimmanci bisa zaton cewa shafin na Ibrahim Bagudu ne.

  Ana sanar da jama'a cewa wannan shafin ba gaskiya bane kuma jama'a su kaurace mashi domin 'dan rito ne sojan gona mai wata manufa ta cuta da bai da alaka da kanin Gwamnan jihar Kebbi Alh Ibrahim Bagudu.

   **************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ibrahim Bagudu a Facebook 'dan rito ne ba shafi na ba ne - Kanin Gwamna Bagudu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });