• Labaran yau

  DSS ta cafke wani mutum bayan ya yi yunkurin sayen kuri'u a zaben Anambra

  Jami'an DSS sun cafke wani mutum da suke zargi da yunkurin sayen kuri'un masu zabe a yayin da ake gudanar da zaben Gwamna a jihar Anambra.Shi dai wannan mutum yana kokarin shawo kan masu kada kuri'a ne da kudi kafin jami'an su cafke shi da ledar kudin.

  Rahotanni sun nuna cewa zaben bai sami halartar mutane da dama ba domin wasu da ya kamata su kada kuri'arsu sun kaurace wa zaben.

  Wata majiya ta shaida mana cewa an ga jirgi mai saukan ungulu na 'yansanda yana shawagi a babban birnin jihar domin sa ido akan abin da ka iya kaiwa ya dawo.


   Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: DSS ta cafke wani mutum bayan ya yi yunkurin sayen kuri'u a zaben Anambra Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama