Nura Bena Daga Gidan Gwamnati |
Gwamnatin jihar Kebbi ta kara jaddada kudirin ta na ci gaba da
hadin gwuiwa da kwararrun likitocin Duniya domin ingata sha'anin kiyon
lafiya ga alummar jihar nan.
Mataimakin Gwamnan jiha Alh. Samaila Yombe Dabai ne ya
bayyana hakan alokacin da yake gabatar da wata kwarya- kwaryar
kyauta ga wasu likitoci da suka yo tattaki zuwa nan jihar Kebbi a
matsayin su na 'yan gida kuma masu kishin jiha domin su bada tasu gudunmawa a sha'anin kiyon lafiya da Gwamnatin ta dauki nauyin gudanarwa a fadin jiha.
Daga cikin su kuwa akwai diyar Mai girma Mataimakin Gwamnan jiha Alh. Samaila Yombe Dabai Watau Dr. Zainab Samaila Yombe
Dabai tare da abokiyata Dr. Maryam.
Dr. Zainab Samaila Yombe Dabai da
Dr. Maryam sun gode wa Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu
akan karamci da aka nuna masu , tare da bada tabbacin goyon bayan su a kowane lokaci
bukatar hakan ta taso domin bada tasu gudunmawa na ciyar da jihar Kebbi gaba.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com