• Labaran yau

  'Dan baiwa,yaro da ke juya kansa ya kalli baya (Hotuna)

  Sameer Muhammad wani yaro ne 'dan shekara 14 wanda ke da wata baiwa da ba kasafai akan sami mai irinta ba, domin Sameer zai iya juya kansa digiri 180 watau zai iya juya kansa ya kalli baya kai tsaye.

  Shi dai wannan yaro 'dan kasar Pakistan ya bar karatun boko tun bayan lokacin da Mahaifinsa ya kamu da rashin lafiya ya kuma shiga wata kungiyar matasa da ke yin rawa da ake kira Dangerous Boys.

  Yaran sukan yi rawa domin a basu kudi, yanayi da Sameer ke dogara da shi domin ya sami kudade da zai kula da iyayensa da sauran kannensa.

  A zantawa da ya yi da wata jarida a kasar Pakistan, Sameer ya ce burin sa shine ya zama jarumi a Masana'antar fina-finai na Bollywood sakamakon baiwar tasa.   Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: 'Dan baiwa,yaro da ke juya kansa ya kalli baya (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama