Budaddiyar wasika ga makiya na ,ni ba dan luwadi bane - Adam A. Zango

Fitaccen jarumin 'dan wasan Fim na Kannywood kuma Mawaki Adam A. Zango ya rubuta wata budaddiyar takarda ga wadanda ya kira Makiyansa. A cikin wasikar Zango ya yi tsokaci akan yadda wadanda ya kira Makiya suka bata masa suna da kokarin ganin sun wulakantar da mutuncinsa.


"Ni ba 'dan Luwadi bane, ko Maroki ko Matsafi.Bana zuwa wajen Malaman tsibbu, bana zuwa wajen wani 'dan Siyasa ko 'dan Kasuwa ko Basarake domin na yi maula.Na yi tawakkali da abin da Allah ya bani.Kuma duk abin da kuka gani a guri na zufa na ne."

 "Abin da kawai zaku yi domin ku hana ni ci gaba shi ne ku kashe ni, kuma baku isa ba domin rayuwa ta a hannun Allah take. Makiya na miye yasa kuke kirkiro karya a kaina, kuna bata suna da mutunci na, na sha gaban ku "

"Kun kira ni Arne, 'dan Luwadi, Mazinaci amma har gobe masoya na suna kauna ta kuma suna sayen Fina Finai da wakoki na. Miye nayi maku ? Duk wanda na taimaka masa domin ya ci gaba sai ya dawo yana neman ya ga bayana"



Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN