• Labaran yau

  Bayar da Auren diyan Yombe su 2, gwarzo ne mara tsoro - Hafsoshi abokan Yombe

  Daga Nura Bena, Isyaku Garba  |

  An bayyana  mai girma mataimakin Gwamnan jihar kebbi, Alh. Samaila Yombe Dabai, a matsayin hazikin Soja gwarzon na miji da bai da tsoro. 

  Wannan yabon ya fito ne daga wasu  Manya sojoji da  kuma  abokan sa a lokacin da suka halarci shedar baikon  'ya 'yan shi biyu da za a gudanar da daurin  aurensu kwanan nan. 

  'Ya 'yan dai na mataimakin Gwamnan  jihar  kebbi ,  Sun had da Rakiyya Samaila Yombe Dabai, da  Basira Samaila Yombe Dabai. 

  Tambayar auren an gudanar da shi ne a Gidan   mai Mataimakin  Gwamnan, jihar kebbi Alh. Samaila yombe Dabai, a unguwar kurmin Mashi da ke jihar kaduna.
  Da yeke amincewa  a madadin Mataimakin Gwamnan , watau Wakilin Zurun Kaduna da kewaye, Alh. Zubairu Kabiru Danjuma, ya ce ya aminta da bada  su baiko tare da yanka masu sadaki kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,  tare da yi masu fatan Alkhairi. 

  Ya kara da cewa ana sa ran gudanar da Daurin Auren a watan gobe watau Disamba in Allah ya kai mu.

  A jawabin sa jim kadan bayan kammala tambayar Auren, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya gode wa dukkanin wadanda  suka halarci gudanar da lamarin, tare da fatan alkhairi ga duk wanda ke da hannu ganin an samu nassarar hakan. 

  Alh. Samaila Yombe Dabai ya kara yana bayyana aure a mastayin daya daga cikin Sunnan Manzon tsira, tare da yin kira ga ci gaba da yin koyi da Manzo (SAW) hadi da yin hakuri da junan su, ganin cewa aure fa ba abin wasa bane. 

   
  Mataimakin Gwamnan na kebbi ya gode wa Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu akan irin shawara , da kuma goyon bayan sa a kowa ne lokaci, tare da dukkanin jama'ar Jihar kebbi baki daya.  

  Haka zalika daga cikin wada da suka amsa tabayoyin manema  labairai a wurin akwai manyan sojin kasarnan  wadan da suka bayyana, Kanal (Col.) Samaila Yombe Dabai, a matsayin haziki kuma  jarumi, a duk inda yake, ba raggo ba ne, na mijin gaske ne, shi ya sa a duk lokacin da lamarinsa ya tashi dole ne su mara masa baya.


  Sun Kara da cewa Jihar Kebbi ta yi sa'a da  samun gwarzo kuma kwararren Gwamna Sanata Abubakar Atiku Bagudu (Matawallen Gwandu) tare da samun haziki kuma  Jarumin mataimakin Gwamna col.  Samaila Yombe Dabai mni,(Tambarin Zuru kuma Turakin Dabai). 

  Sauran wadanda suka yi jawabi a wurin sun hada da Wakilin Zurun kaduna da Kuma Shugaban karamar hukumar mulki ta Yauri Alh. Musa stone hadi da Alh. Dan musa  Ribah dukkaninsu sun nuna jin dadin su akan sha 'anin bada auren.

  Haka Kuma sun shawarci ma auratan da su yi hakuri da junan su da  fatan Allah yasa wa auren da za ayi Albarka. 
  Cikin wadanda suka samu halarci lamarin sun hada da manya tsoffin Soji na sama da na kasa a ciki da wajen kasarnan.  

  Sauran mahalarta sun hada da wasu manya daga Majalisar dinkin Duniya UN da na DAFUR hadi da  na hukumar  Dept.of Safety and Sec. Abuja da maiduguri.


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Bayar da Auren diyan Yombe su 2, gwarzo ne mara tsoro - Hafsoshi abokan Yombe Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });