• Labaran yau

  Barawo ya mayar da kayan sata bayan kudan zuma sun lullube shi (Hotuna)

  Wani ibtila'i ya sami wani matashi a garin Misindi na kasar Uganda sakamakon kudan zuma da suka dabaibaye shi suka yi ta harbinsa bayan ya saci wani kayan kida Woofer daga wajen wani mutum.

  Lamarin ya sa ala tilas matashin ya mayar da Woofer da ya sata yayin da kudan zuman suka makale a jikinsa har zuwa wajen da ya sato wannan Woofer.

  Idan baku manta ba ,kwanakin baya mun kawo maku labarin wani mutum da kudan zuma suka lullube hannun sa na dama bayan ya saci wata mota sanadin da ya sa ala tilas shi ma ya mayar da motar.

  Haka zalika wata da ya gabata mun kawo maku labarin wadansu samari biyu da suka tsayar da motar da suka sata suka fito suka tube zindir suka yi ta sheka rawa a fili gefen titi da rana kiri kiri duka a kasar ta Uganda.  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Barawo ya mayar da kayan sata bayan kudan zuma sun lullube shi (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama