• Labaran yau

  Baiwar Allah da ta shake jariri har ya mutu awowi kadan bayan ta haife shi (Hotuna)

  Wata mace mai suna Miss Oloho 'yar shekara fiye da 20 wacce wada ce mai lankwasassun kafafu wacce ke zaune a No 1 omohwovo street,Iwhrekpokpo a karamar hukumar ughellina ta Arewa ta kashe jariri da ta haifa 'yan awowi kadan bayan ta haife shi.

  Olohoh wacce ke sana'ar sayar da soyayyen busashen plantain ta haifi jaririn nata ne da yammacin Talata ba tare da samun taimako daga kowa ba. Amma kukan jaririn ya sa makwabta suka zo suka taimaka mata tare da bayar da taimako ciki har da suturar jarirai saboda Oloho bata tanadi komai ba kafin haihuwar jaririn.

  Bayanai sun nuna cewa lokacin da makwabta suka dawo da safe domin su ga jariri sai Oloho ta shaida masu cewa ai mahaifin jaririn ya zo ya dauki jaririn da dare bayan ya kula cewa jaririn baya nufashi da kyau.Kasancewa makwabta basu gamsu da bayanin Oloho ba sai suka tambayi wani 'dan karamin yaro wanda kanin Oloho ne domin duk wannan abin da ke faruwa mahaifan Oloho basu gida sai dai ita da kannen ta.

  Yaron ya gaya wa makwabta cewa bayan da suka bar su da dare, Olohoh ta tafasa ruwan zafi ta dura ma jaririn, amma sai jaririn bai mutu ba, daga bisani ta dauko kyalle ta daure hanci da bakin jaririn daga bisani jaririn ya daina motsi. 'Dan karamin yaro ya ci gaba da cewa gani haka ya sa ta dauki jaririn ta saka a cikin wani laida kuma ta hada da sharan 'bawon plantain a cikin laidan da ta saka jaririn sai ta kira wani mai tabin hankali ta bashi ta ce ya je ya jefar a bola.

  Jin wannan jawabi daga bakin kanin Olohoh wanda 'dan karamin yaro ne sai makwabta suka bazama bincike bola bola inda daga bisani suka gano laida da ta saka jaririn a ciki kuma da suturar da makwabta suka bata sanye a jikin jaririn amma ya riga ya mutu.Alamu su nuna a bakin jaririn yadda bakinsa ya kone sakamakon ruwan zafi da Olohoh ta dura masa, haka zalika alamu sun bayyana a wuyan jaririn na makura ka shakewa.

  Yanzu haka an mika wanna baiwar Allah a hannun hukumar 'yansanda na shiya ta B da ke Ughellina na jihar ta Delta.Har yanu dai mahaifan Oloho basu bayyanna ba a wajen 'yansanda haka zalika ta ki ta fada ko waye ya yi mata ciki.


  **************************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Baiwar Allah da ta shake jariri har ya mutu awowi kadan bayan ta haife shi (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });