• Labaran yau

  B-kebbi: An bude gasar wasan kwallon kafa na cin kofin Gwamna Atiku Bagudu

  Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai a babban filin wasa da ke Sakatariyar Haliru Abdu da ke cikin garin Birnin kebbi ya bude bikin wasan kwallon kafa  na manyan Makarantu da NYSC don  cin Kofin Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

  Waziri Umar Federal polytechnic Birnin Kebbi da Federal University Birnin Kebbi sune suka fara buda wasar da fafatawa a wasan kwallon kafan, daga bisani Federal University Birnin Kebbi
  ta tashi da ci biyu yayin da Umar Federal polytechnic Birnin Kebbi na da ci daya.

  Baya ga Mataimakin Gwamna Samaila Yombe Dabai wadanda suka sami halartar bikin sun hada da Kwamishinan Filaye da Gidaje Alh. Abubakar Cika Ladan da Kwamishinan Kudi Alh. Zaki Kambaza da Kwamishinan ilimi Mai Zurfi Alh. Maigari Dakin Gari da Kwamishinan Wasannin Alh. Abubakar Imam Besse da Alh. Kabiru Nabade da P. A. Na Maigirma Gwamnan jihar Kebbi Alh. Faruku Musa Yaro Enabo tare da suran jama'a da 'yan wasa na kungiyoyi da dama.

  'Yan wasan gargajiya daga Masarautar Zuru sun nishadantar da masu kallo da kade-kade da raye-raye tare da 'yan wasa na NYSC.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: B-kebbi: An bude gasar wasan kwallon kafa na cin kofin Gwamna Atiku Bagudu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });