Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyar APC

Tsohon shugaban kasa zamanin shugaba Olusegun Obasanjo watau Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar mai mulkin Najeriya APC a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a.

A cikin takardar sanarwar, Atiku Abubakar ya zargi jam'iyar APC mai mulki da gaza cika alkawarin da ta dauka na canja rayuwar 'yan Najeriya wanda shine ginshikin alkiblar yakin neman zabe a 2015.

Ya kara da yin bayani akan abin da ya kira "yadda dangantaka ya yi kamari tsakanin jiga-jigan 'yan jam'iyar ta APC  da aka kasa daidaitawa kuma hakan ya haifar da babban gibi na rashin fahimta a cikin 'ya'yan jam'iyar".

Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya taba danganta Atiku Abubakar a matsayin mutum da baya da alkibla kuma mai kwadayin mulki ko ta halin kaka, Obasanjo ya kara da cewa zaben Atiku zai kasance babban kuskure da 'yan Najeriya za su yi a kasarsu.

Amma wani hadimin Atiku Abubakar ya mayar da martani a zancen na Obasanjo a waccan lokacin cewa Obasanjo mutum ne da baya da godiyan Allah kuma mutum ne da ke bakin ciki da ci gaban wasu ta hanyar sa ido akan abin da bai kamace shi aba.

Yanzu da hakan ta kasance, miye kenan zai kasance alkiblar siyasar Abubakar Atiku, ya yi murabus ne a harkokin siyasa ko kuwa zai koma gidan da ya fice babu sallama ta jam'iyar PDP ko kuwa zai kirkiro wata sabuwar jam'iya ce ?...Lokaci ne kadai zai tabbatar da haka.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN