• Labaran yau

  An kama wacce ta jefa jariri da ta haifa 'dan kwana 1 a cikin masai

  Hukumar 'yansanda a jihar Katsina ta kama wata mace mai suna Shamsiya Hassan da ake zargi da jefa jariri da ta haifa mai kwana daya a Duniya cikin masai wanda sakamakon haka jaririn ya mutu a garin Funtua na jihar ta Katsina .

  Yayin da take yi wa Manema Labarai jawabi ranar Juma'a a Hedikwatar 'yansanda na jihar Katsina, Shamsiya ta ce ita bata san cewa jariri ne ya fado daga cikin mahaifarta ba.

  Bayanai sun nuna cewa wannan ya faru ne kwana daya bayan ta tare a gidan sabon Angon ta wanda yake tababa akan yanayin ta tun farko.

  Ita dai Shamsiya tana zaune a rukunin gidaje na Nassarawa ne da ke garin Funtua kafin faruwar lamarin.

  Wani makwabci da ya ji kukan jariri a masai bayan Shamsiya ta fito shi ne ya ankarar da jama'a akan lamarin da ya kai ga gano tare da ceto jaririn daga cikin masai amma daga bisani ya mutu.

  'yansanda sun kama saurayin ta mai suna Jamilu wanda shi ma mazauni garin Funtua ne. Shamsiya tana da yara biyu kafin aukuwan wannan lamarin bayan ta rabu da mijin ta na farko.

  Kakakin rundunar 'yansanda na jihar Katsina Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma kara da cewa hukumar za ta gurfanar da Shamsiya da Jamilu a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kama wacce ta jefa jariri da ta haifa 'dan kwana 1 a cikin masai Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });