An gudanar da taron Arewa maso yamma na APC Social Media Forum a karon farko

Daga Wakilin mu |

A karon farko a tarihi , shugabannin kungiyoyin social media na jahohin arewa maso yamma da suka  kunshi Sokoto, Kebbi, Katsina, Kano, Kaduna, Zamfara, da kuma Jigawa sun gudanar da taron su a wannan rana ta lahadi 12-11-2017 domin kafa wani kasaitaccen forum da zai hada hancin kungiyoyin da sunka fito daga wadan nan jahohin.

Taron wanda ya gudana a jahar Sokoto, ya samu halartar dukkan shugabannin kungiyoyin (In banda kaduna), inda aka tattauna muhimman batutuwa da zasu taimaka wajen habbaka ayukkan  wadan nan kungiyoyin, habbaka jam'iyyar APC da Gwamnatocin jam'iyyar da suke cikin wannan yankin, hadi da Gwamnatin tarayya.

Cigaban da aka samu da kalubalen ayukkan social media a wadan nan jahohin na daga cikin batutuwan da suka mamayen taron inda kowane chairman ya zayyano cigaban da kungiyar sa da jahar sa suka samu a sha'anin social media.

A wurin taron, an ayyana Engineer Adamu Attahiru daga jahar Kebbi a matsayin shugaban riko na wannan kungiya, yayin da Alh. Dahiru Mani daga jahar katsina ya zama sakataren sa.
Daga cikin chiyamoman da suka halarci taron sun hada da :

1.  Engineer Adamu Attahiru - Chairman Kebbi State APC Social Media Organization._
2.  Ahmed Rufa'i Gummel - Chairman Jigawa State APC Social Media Organization._
3.  Alh Dahiru Mani - Chairman Katsina State Social Media Organization_
4.  Nuraddeen Harande Mahe - Chairman, Sokoto State Social Media Organization_
5.  Auwal Kingdom - Chairman, Kano State Social Media Forum_
6.  Ibrahim Bello Gusau Ibg - Chairman, Zamfara State APC Social Media Organization._

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN