• Labaran yau

  An ceto yara 30 daga hannun barawon yara (Hotuna)


  'Yansanda a Kafanchan na jihar Kaduna sun kama wani mutum wanda ya dade yana rudin yara kanana da alawa da biskit daga bisani sai ya sace su.

  Bayan da asirin wannan mutum ya tonu,ya kai jami'an 'yansanda wani gida a Gwagwalada na birnin Abuja inda 'yansandan suka kama wata mata tare da wasu mutum biyar wadanda ke yi wa matar aiki bayan sun gane cewa a gidan ne ake ajiye yara da aka sato daga bisani sai matar ta sayar da su ga mabukata.

  An gano akalla yara 30 a gidan kuma hukumar 'yansanda ta bukaci wadanda yaransu suka bace su hamzarta zuwa chaji ofis na gwagwalada domin shaida yaransu.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: An ceto yara 30 daga hannun barawon yara (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama