• Labaran yau

  'Yar shekara 3 ta mutu bayan 'dan shekara 50 ya yi mata fyade

  Rashin wadataccen imani da tausayi sai kara samun gindin zama yake yi a cikin zukatan wasu bayin Allah kamar yadda ta kasance da wani mutum mai suna Abdullahi Sani 'dan shekara 50, Abdullahi ya rudi wata karamar yarinya mai shekara uku kuma ya kaita wani kangon gida yayi mata fyade lamarin da ya kai ga zama ajali ga yarinyar mai suna Umma Ibrahim a Jabiri na karamar hukumar Funtua a jihar Katsina.

  Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Katsina DSP Gambo Isah yace wanda ake zargin ya aikata wannan danyen aiki ne bayan ya rudi yarinyar zuwa wani kangon gida gurin da ya yi mata fyade.Daga bisani an kai yarinyar babban Asibitin Funtua amma yarinyar ta rasu washegari sakamakon raunuka da ta samu yayin da Abdullahi  yayi mata fyade.

  Abdullahi Sani wanda aka fi sani da suna Mai Aya ya amsa laifinsa a gaban 'yansanda yayin da kakakin hukumar 'yansanda yace za su gurfanar da Abdullahi a gaban Kotu da zarar sun kammala bincike.   Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yar shekara 3 ta mutu bayan 'dan shekara 50 ya yi mata fyade Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });